Home Labarai MATAR MUTUM KABARINSA: Ɗan bautar ƙasa ya yi baiko da macen soja a sananin NYSC

MATAR MUTUM KABARINSA: Ɗan bautar ƙasa ya yi baiko da macen soja a sananin NYSC

0
MATAR MUTUM KABARINSA: Ɗan bautar ƙasa ya yi baiko da macen soja a sananin NYSC

 

Wani fefen bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa ya nuna wani ɗan bautar ƙasa ya na yin baiko ga wata macen soja a sansanin horon masu bautar ƙasa, NYSC da ke Yikpata a Jihar Kwara.
A fefen bidiyon, an ga ɗan bautar ƙasar da har yanzu ba a kai ga gano sunan shi ba, ya na riƙe da zobe, ya kuma durƙusa kan gwiwoyin sa a gaban sojar, inda ya jefa mata tambayar ko za ta aure shi?, ai kuwa ba ta yi wata-wata ba ta kada baki ta ce eh!, ta yarda.
Sai kuwa ɗan bautar ƙasar ya miƙe tsaye, ya sanya mata wannan zobe a ɗan-yatsa, ita kuma sojar baki ya ƙi rufuwa, inda waɗanda ke wajen su ka riƙa shewa da tafi.
Jaridar Cable ta rawaito cewa, a bidiyon an ga sojar ta na cike da murmushi har ta na sumbatar zoben da ɗan bautar ƙasar ya saka mata a ɗan yatsa.
A ɗaya fefen bidiyon kuma an ga masoyan biyu na tsinkar furen soyaiya, in da har ya saka hularta ta sojoji yayin da ita kuma ta ke tsaye a bayan shi.
Daga bisani kuma su ka sumbaci junansu, lamarin da ya sanya sauran ƴan bautar ƙasa su ka ɓarke da sowa da tafi.
Cable ta rawaito cewa har yanzu dai ba a kai ga gano yadda soyaiya ta ɓarke a tsakanin masoyan ba.