
Wani matashi mai shekaru 17 da mai shekaru 27, sun rasu a wani ramin masai da ke Kasuwar Sabon Gari a Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar Kano a jiya Asabar, yayin da ya bude ramin.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a Kano a yau Lahadi, inda ya ce hatsarin ya faru ne cikin dare.
Ya bayyana cewa matashin mai shekaru 27 a duniya yana aiki ne a cikin ramin lokacin da ya makale kuma a kokarin ceto shi abokin aikinsa, matashi mai shekaru 17 ya shiga cikin babban ramin mai fadi kuma shi ma ya makale.
“Mun sami kiran gaggawa a kan hatsarin kuma nan da nan mu ka aika da tawagar ceto zuwa wurin,” in ji shi.
Ya kara da cewa hukumar kashe gobara ta fitar da matasan a sume, inda su ka kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda likitocin da ke bakin aiki su ka tabbatar da mutuwar su.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa an mika gawarwakin ga ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari.
Ya danganta mutuwar mutanen da yawan zafin cikin ramin da kuma rashin iska