Home Labarai Matashi ya ɓata shekaru 3 bayan ɓacewar yayansa da har yanzu ba a ganshi ba a Kano

Matashi ya ɓata shekaru 3 bayan ɓacewar yayansa da har yanzu ba a ganshi ba a Kano

0
Matashi ya ɓata shekaru 3 bayan ɓacewar yayansa da har yanzu ba a ganshi ba a Kano

 

 

Wani matashi ɗan shekara 16, mai suna Idris Auwal ya ɓata a jihar Kano.

Shi dai Auwal, wanda a ka fi sani da Amir, ya ɓata ne tun ranar Alhamis, shekaru uku kenan bayan da yayansa uwa ɗaya uba daya, Abdullahi Auwal mai shekara 17 shi ma ya ɓata kuma har yanzu ba a ganshi ba.

Auwal, mazaunin unguwar Hotoro, ya bar gida ne da misalin ƙarfe 2 na rana bayan da ya ɗebo ruwa a bokiti zai yi wanka

Mahaifiyar Auwal, Shema’u Idris, wacce ta ke cikin ɗimuwa da tashin hankali, ta shaida wa wakilin Daily Nigerian Hausa cewa wasu a unguwar ma sun ga fitar da daga gida amma kuma har yanzu bai dawo ba.

A cewar ta” ya ɗebo ruwa kenan da misalin ƙarfe 2 na rana zai yi wanka, sai ya ce wa sauran ƴan uwansa yana zuwa amma har yau bai dawo ba.

“Shekaru uku kenan cif da batan yayansa ɗan shekara 17. Ina cikin wani hali kuma ni duk inda ya dace mu je, mun je amma Allah bai nufa mun gan shi ba.

“Dan Allah ina kira ga hukumomi da su taimaka min wajen nemo yaron nan,” in ji Shema’u.