
A jiya Alhamis ne wani matashi mai suna Kingsley Paul, mai shekaru 24 da haihuwa ya hau ƙololuwar ɗaya da ga cikin fitilun cikin wasan ƙwallon ƙafa na UJ Esueneda ke birnin Calabar a jihar Cross Rivers domin ya nuna fushin sa kan lalacewar filin wasan.
Paul, ɗan aji 4 a Jami’ar Calabar, ya taki sa’a jami’an ƴan sanda na sashen yaƙi da garkuwa da mutane da ƙungiyoyin asiri sun sakko da shi.
Ya ce izzar Ubangiji ce ta sa shi ya yi hakan domin nuna fushin sa.
A cewar sa, shi ba ɓarawo ba ne kuma bai yi hakan ɗin ya kashe kansa ba, inda ya ƙara da cewa ya yi hakan ne domin ya jawo hankalin hukumomi a kan halin ƙaƙanikayi da filin wasan ya tsinci kan sa.
“Duk da dai na ga an gyara gurin ninƙaya da filin ƙwallon kwando. Amma sauran ƴan wasa su na shan wahala sabo da hanyar tsere na filin wasan a lalace ta ke,” in ji shi
Paul ya ƙara da cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin yanka hankalin gwamnati ta gyara, inda ya ce abinda ya yi wani salo ne na sanyawa hankali ya kai kan filin wasan.
Lamarin ya haifar da cunkoson ababan hawa a titin Murtala Mohammed, inda wasu masu Aban hawa su ka riƙa sauya hanya.