
Wani mai goyon bayan jam’iyyar Labour Party ta Nijeriya, wanda a ka bayyana sunansa da OGersh, ya hau ƙololuwar dutse mafi tsayi a Afirka, Dutsen Kilimanjaro ya dasa tutar jam’iyyar a can.
Jaridar Punch ta rawaito cewa OGresh ya yi tafiya ta tsawon sa’o’i 10 da rabi zuwa saman dutsen, wanda ke a ƙasar Tanzania domin kafa tutar jam’iyyar a dandalin Uhuru Peak.
Dutsen da ke Uhuru Peak shine mafi tsayi a Afirka, inda 4ahotanninsubka tabbatar da cewa har aman wuta ya ke yi a wasu lokutan.
OGersh ya wallafa hotonsa a Uhuru Peak, kusa da tutar jam’iyyar Labour a jiya Talata, ya na mai cewa, “A ranar Juma’a, 20/10/2022 bayan awa 10½ na hawan dutse da kuma yawon buɗe-ido.
Na kai ga ƙololuwar dutsen Uhuru Peak, wato Dutsen Kilimanjaro, mai tsayin mita 5,895 sama da teku.
“Babu wani wuri mafi kyau don sanar da zuwan sabuwar Najeriya fiye da rufin rufin Afirka,” in ji shi