Home Labarai Matashi zai biya diyyar N52m bisa yi wa wani rauni har ta kai ga an yanke masa hannu a Kano

Matashi zai biya diyyar N52m bisa yi wa wani rauni har ta kai ga an yanke masa hannu a Kano

0
Matashi zai biya diyyar N52m bisa yi wa wani rauni har ta kai ga an yanke masa hannu a Kano

 

 

 

A juya Juma’a ne dai wata Kotun shari’ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a jihar Kano ta yanke wa wani sami matashi mai suna Abubakar Ayuba, ɗan kimanin shekaru 20 da haihuwa da laifin yiwa wani Salisu Usaini mummunan rauni a hannu, har ta kai ga hannun ya ruɓe a ka yanke shi a asibiti.

Laifin, a cewar alƙalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya saɓawa sashi na 159 na kundin dokar laifuka (Penal Code) ta jihar Kano.

Shi ya sa alkali Ahmad ya yanke wa mai laifin hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari da kuma biyan diyyar Naira Miliyan 52 da dubu 970 a cikin shekaru ga mai ƙarar.

Alkalin ya kuma umarci wanda a ke ƙara da ya biya Naira dubu 650 kuɗin magani da wanda ya shigar da ƙara ya yi tun daga farkon jin raunin har zuwa warkewar sa.

Tun da fari dai, a ranar 20 ga watan maris, 2022 aka zargi Abubakar da daukar wata sharɓeɓiyar wuka ya kuma kaftawa matashi Salisu Usaini a hannunsa na dama, kuma dalilin wannan aika-aikar da Abubakar din yayine ya janyo likitoci suka tabbatar da cewar babu shakka sai dai a guntule hannun, saboda tuni hannun ya ruɓe.

Koda likitoci suka cire hannun matashin, sai fa hannu ya cigaba da ruɓe wa har sai da hakan ya sanya aka sake yi masa aiki, daga karshe kuma sai da aka guntile hannun gaba daya tun daga allon kafadarsa.

Da a ka kai mai laifin kotu, mai gabatar da ƙara, Aliyu Zainul Abideen ne ya karantawa matashin tuhumar da aike yi masa, tun kuma a wancan lokaci Abubakar ya amsa wannan zargi da a ke yi masa.

Hakan ne ya sanya kotun ta umarci jami’an gidan gyaran hali da su ajiyeshi har sai anga yanayin halin da mara lafiyar yake ciki.