
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen hawa ta Jihar Kano, KAROTA tayi nasarar cafke wani matashi yana sojan-gona da sunan shi Jami’in hukumar KAROTA ne.
A cewar mai taimakawa shugaban hukumar kan harkokin kafafen yada labarai na zamani, Ayuba Jarumi, KAROTA ta cafke matashin ne da misalin karfe 12 na daren litinin, dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci akan titi yana karɓar kudi.
Matashin, mai suna Lukman Abdullahi, mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabongari, bayan ya shiga hannu, ya bayyana wa KAROTA cewar shi ɗan Maiduguri ne.
Ya ƙara da cewa yana amfani da kayan ne saboda jama’a su fahimci shi ma’aikacin hukumar KAROTA ne.
Ya ce dama chan hukumar ta jima tana samun Rlrahoton yadda matashin ke amfani da sunanta wajen musgunawa al’ummar Jihar Kano, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.
Daga karshe shugaban Hukumar ta KAROTA, Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma.
Ya kumace da zarar hukumar ta kammala bincike akansa za ta miƙa shi hannun jami’an Ƴan sanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.