
Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya bayar da umarnin kama duk wanda ya ki karban tsoffin takardun kudi na naira dari biyu da dari biyar da dubu daya a jihar.
Ya ce tsohon takardun kudin na nan a kan doka har sai an yanke hukunci na karshe a kan babban bankin Najeriya (CBN) da gwamnatin tarayya da gwamnoni uku na jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara su ka shigar a kotun koli.
Matawalle ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da sabbin alkalan babbar kotuna da sabbin masu ba da shawara na musamman da aka nada a gidan gwamnati da ke Gusau babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, shi da takwarorinsa na jihohin Kogi da Kaduna sun garzaya kotun koli don ba da umarnin tsawaitawa wa’adi da tabbatar da ci gaba da amfani da tsohon takardun kudi na Naira 200, 500 da 1000.
“Kamar yadda kuka sani, tattalin arzikin kasar nan gaba daya ya fada cikin mawuyacin hali sakamakon matakin da babban bankin kasar ya dauka na dakatar da amincewa da tsohon takardun Naira a matsayin takardar kudi daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
“Wannan matakin ya kara sanya tabarbarewar halin da jiharmu ke ciki na ta’addanci da aikata laifuka daban-daban, wadanda su ka kawo cikas ga harkokin tattalin arziki a jihar da kuma yankin tsawon shekaru,” in ji Gwamna Matawalle.