Home Labarai Matsalar tsaro da ambaliyar tasa manoma 46, 000 rasa muhallin su a Niger

Matsalar tsaro da ambaliyar tasa manoma 46, 000 rasa muhallin su a Niger

0
Matsalar tsaro da ambaliyar tasa manoma 46, 000 rasa muhallin su a Niger

Jimillar manoma 46, 853 daga gidaje 5, 863 ne suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan yan fashin daji da ta’addanci da ambaliyar ruwa da rikicin makiyaya da manoma a fadin jihar Niger.

Wani rahota da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger ta samu ya nuna cewa wasu daga cikin manoman sun rasa muhallinsu sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji tun 2018.

Bayanan sun nuna cewa manoman da abin ya shafa sun hada da maza 5, 863 da mata 23, 450 da kananan yara 17, 740.

Hukumar ta ce akwai ‘yan gudun Hijrah 5, 823 a sansanin ‘yan gudun Hijrah na Gwada da ya hada da maza 970 da mata 2, 051 da kananan yara 2, 802.

A sansanin ‘yan gudun Hijrah na Kuta, hukumar NSEMA ta bayyana cewa akwai manoma ‘yan gudun Hijrah 3, 180 wadanda ya hada maza 530 da mata 1, 040 da kananan yara 1, 610 inda ta ce an bude dukka sansanonin a 2018.