Home Labarai Matsalolin da suke damun da yawan ‘yan mata a wannan zamanin

Matsalolin da suke damun da yawan ‘yan mata a wannan zamanin

0
Matsalolin da suke damun da yawan ‘yan mata a wannan zamanin
Aisha Sadiq Chuchu
Daga Aisha Sadiq Chuchu
Wani shiri na kalla a gidan talabijin din Joy Prime ta ƙasar Ghana akan zamantakewa mai suna Home Affairs. Su kan gayyato masana a bangaren zamantakewa don a tattauna da su akan wani maudu’i, su kuma bada shawara.
Ana tsaka da shirin ne wani ya kira waya yana koken yadda budurwarsa ta cika roƙonsa kuɗi, shi kuma yana sonta.
Abinda ya ja hankalina na kawo batun anan ba komi bane face tabbas akwai mata masu irin wannan halayyar na yawan roƙon maza, wasu su na son samarin na su amma son abin hannun samarin ya rinjaya,sai saurayi ya kasa bambamce shin da gaske shi ďin a ke so ko abin hannunsa. Akwai wadanda su dama abin hannunka su ke so,soyayyar ka a gare su ba ta ďaďa su da ƙasa ba, sai bukatar su ta taso zasu neme ka da kuma sun sami abinda su ke so,shikenan sai su watsar da kai,sai kuma buƙatar hakan ta taso.
Duk yanda saurayi ya kai ga son budurwa ba zai so mai takura ma sa ba,irin haka daga saurayi ya ga kiran budurwa sai hankalinsa ya tashi, yayi ta fargabar daukar kiran saboda ya san maganar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.
Ya kamata mata su lura da cewa shi fa namiji ba injin ATM ba ne da a kowane lokaci ake tatsar kudi a wajensa, ko ATM akwai loton da yake sa “Unable to dispense cash ” ko “out of service “. Kunga kenan injin Nasara kenan da aka ƙera dan wannan amfanin. A matsayinki na mace ya kamata ki fahimce cewa mazan nan kala-kala ne, sannan kowane da irin ƙarfinsa wajen samu. Tun farko ma idan namiji mai bayarwa ne  za ki gane cewa shi mai bayarwa ne, haka nan kuma idan dunƙulallen hannun gare sa za ki gane daga yanda ku ka fara. Sannan hali ya bambamta wani ko baya da shi yana da kyauta, wani kuwa ko yana da shi be iya kyauta ba sam.
Wannan kyautar da saurayi zai ba budurwa ki sani cewa kyautatawa ce tsakaninku dan ya ba ki kudi ko ya siya ma ki wani abu, idan ya ba ki ki karba da hannu biyu idan be ba ki ba kar ki roka akwai zubar da kima yin hakan, kin nuna gazawar mahaifanki da nauyin dawainiyar ki ya rataya akansu. Babu inda aka ce dole ne sai ya ma ki kyauta,sai dai mi? Ita kyauta na karfafa soyayya,ba wai ga namiji kadai ba, har da ke mace idan san samu ne, komin ƙanƙantar abu ki ba shi, hakan zai ƙara danƙon so a tsakaninku.
Ta wata fuskar kuma akwai mazan da wannan kyautar ba ta dame su ba, koda su na da halin yi, akwai matan da ke da kunyar su bude baki su roki namji kudi, ko da mahaifinsu ne ko dan uwansu, sai dai su kan nuna ma haske ta hanyar maganganunsu, irinsu daga nan za ka fahimci abinda suke so.
Misali wata za ta iya cewa “Kasuwa nake son zuwa, ko na so kiran ka dazu ashe ba kati a wayar” da makamanta irin wadannan. Kana jin haka ka san maganar kudi ce idan kana da halin yi kayi, idan ba ka da shi ka hakura.
Yanzu soyayya ta zama kamar gasa, wani a shirye yake da ya kashe ma budurwarka ko nawa ne dan ya samu koda rabin son da take ma ka ne, kai kuma kana nan ka tsaya sanya,kana ganin tunda tana son ka ba ka da matsala.
Mata nada rauni, wata abu ƙanƙani sai ya juyar ma ta da tunani, ta kasa gane abinda take so. Sai kaga cikin ƙanƙanin lokaci ta juya ma baya saboda wani, kayi ta tunanin ta daina sonka, bayan a ƙasan zuciyarta kai ɗin take so,amma son abin duniya yasa ta guje ka saboda ba ka ma ta abinda wane ke yi ma ta.
Jan hankali ga ƴan uwa  mata ya kamata su guji nuna maitar su a fili na son abin duniya. Kar ki bari abun duniya ya rude ki, ki saki reshe ki kama ganye,wani ba sonki yake ba tsakaninsa da Allah ba wani abu na ki yake so, akwai maza irin wadannan dan abu ne da ke faruwa yana kuma kan faruwa, ke daga yanda namiji ke faman kashe ma ki kudi haduwar farko ba dangin Iya ba na Baba haba! Ai ya dace ki dau haske,ki gane inda ya dosa. Duk namijin da ke sonki da gaskiya haɗuwar farko ba zai dauko maƙuɗan kuɗaɗe ya ba ki ba, irin wadannan kuwa abin da za su fara jawo hankalinki da shi kenan, idan an yi sa’a dama ke kwaɗayayya ce burin shi ya cika, daga nan kin shigar kan ki cikin halaka.
Iyaye ma na bada ta su gudunmuwar wajen cusa ma ƴaƴa mata ɗabi’ar son abin duniya, musamman iyaye mata. Wata uwar da kanta za ta nuna ma yarinya wane da wane basu dace da ke ba. Abin mamaki tun tasowa ake cusa wannan ɗabi’ar a zuciyar yara mata, daga yarinya ta fara tasowa za a ji iyaye na faɗin ai wance matar gwamna ce, haka za su riƙa ambaton manyan muƙaman gwamnati ma su riƙe da madafun iko. Tun daga nan yarinya ta sa a ranta cewa talaka ba sa’an aurenta ba ne, ita ta wuce da ajin sa alhali ita ɗin ba ɗiyar kowa bace.
Daga nan ba ta sauraren kowa sai mai kuɗi, mai kuɗin ma burinta mi za ta samu a wajensa.
Akwai iyayen da za su tura ɗiyar su makaranta ba tare da kuɗin da za ta yi hidimar gabanta ba, shin sana’a take yi ko sata su ka tura ta yi? Idan ba ta san a’a to tabbas sun jefa ƴar su cikin halaka, shiyasa ake samun mata masu zaman kansu da yawa a makarantun gaba da sakandire. Ku iyaye ba ku ba yarinya kuɗi ba, ba ku siya ma ta ba sai ku ganta da babbar waya, sutura ta kece raini, amma ba za ku buɗe baki ku tambaye ta ba, musamman ita uwa da ke tare da yarinyar, daga nan uwa za ta fara murna ai ɗiyarta tayi goshi.
Sun manta cewa su fa ƴaƴa amana ne a hannunsu, gangancin da iyaye keyi a wannan zamanin dangane da yara mata ba kadan bane, ba ruwan su da sauke nauyin da ya rataya a kawunansu burinsu a ce ɗiyarsu na mu’amala da masu kuɗi. Ita kuma yarinya idan ba ta kai zuciyarta nesa ba shi kenan ta gama yawo ba ta da mai kwaɓa ma ta,abin da ta ga dama shi za ta yi, wata ma idan ta bunƙasa ita ke daukar nauyin iyayenta.
Ya kamata iyaye su lura da ƴaƴansu, su yi bakin ƙoƙarinsu wajen kula da tarbiyyar yaran su, musamman uwa da ke zaune da yaran a gida. Ya kamata ki san shiga da ficen ɗiyarki wane saurayi ta ke da shi, ƙawayenta. Idan kuɗ ki ka ga tana kashewa ki san daga ina suka fito. Tarbiyya a hannun iyaye ta ke, shiriya kuwa ta Allah ce, ku gwada ma yaran ku tsoron Allah a duk inda suke, shi zai taimake su, ku kuma bi su da addu’a, kar ku cusa ma su dogon buri a zukatansu.
Aisha A. Sadiq (Chuchu)