Home Labarai Matsalolin Nijeriya: Gyaran kundin tsarin mulki ne kawai mafita — Kawu Sumaila

Matsalolin Nijeriya: Gyaran kundin tsarin mulki ne kawai mafita — Kawu Sumaila

0
Matsalolin Nijeriya: Gyaran kundin tsarin mulki ne kawai mafita — Kawu Sumaila

 

 

 

Tsohon Mataimakin Shugaban marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Abdulrahaman Kawu Sumaila ya bayyana cewa akwai buƙatar a sake duba kan kundin tsarin mulkin Najeriya cikin gaggawa, inda ya ce hakan zai magance yawancin kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

Sumaila ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.

Yace shekaru goma 12 da ya yi a majalisar a karkashin shugabannin Kasa guda 3, ya sa ya fahimci cewa Najeriya na bukatar tsarin da zai taba rayuwar al’umma tun daga tushe Inda yace baiwa Kananan Hukumomi damar cin gashin kansu ita ce mafuta.

Sumaila wanda ya kuma yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan majalisar wakilai ta kasa, ya ce, a fahimtarsa akwai matsaloli da yawa da kundin tsarin mulkin kasar nan ya haifar kamar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da matsalolin zamantakewa wanda yace akwai bukatar a sake duba kundin tsarin wanda zai yi dai-dai da buƙatun al’ummar Kasa, wanda ya kira d “Tsarin Mulkin Jama’a”.

Sumaila, ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin jam’iyyar NNPP ya ce idan ya lashe zaɓen, zai mayar da hankali wajen gyaran kundin tsarin mulki da kuma yi masa kwaskwarima.

“Idan na zama dan majalisar dattawan Najeriya, zan dage wajen ganin an yiwa kundin tsarin mulkin kasar cikakken nazari da kuma gyara.” Kawu Sumaila

“Kasa mai yawan al’umma kamar Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 200 ace tana da Babban sufeton ‘yan sanda guda daya ko shakka babu dole za’a fuskanci kalubalen tsaro”. Inji Kawu.