
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara tsaunin Mambila dake yankin karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba kafin ya tashi zuwa Accra babban birnin kasar Ghana a yau.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, a yau Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon zababben Shugaban kasar Laberiya George Weah a fadar Gwamnati dake Abuja kafin isarsa jihar Taraba.
Tuni dai hadiman Shugaban kasa na musamman suka isa jihar Taraba domin shirya yadda za’a karbeshi a yayin wannan ziyara da zai kai akan hanyarsa ta zuwa kasar Ghana.
NAN ta tabbatar da cewar bayan ya isa jihar Taraba, Shugaban kasa zai kai ziyarar gani da ido inda aka kai hare hare a ‘yan kwanakin nan, zai kuma gana da Sarakunan gargajiya na yankunan tare da masu ruwa da tsaki a jihar domin samo bakin zaren rikita rikitar da jihar ke fama da ita.
Rikicin baya bayan nan dai shi ne wanda aka yi a tsaunin Mambila wanda aka kashe akalla mutane 20 tare da sace ko kashe a kalla shanu 300.
Tsaunin mambila dai ya jima yana fuskantar irin wadannan rigingimu da sukan kai ga hasarar rayuka, inda daruruwan mutane suka mutu a baya bayan nan.
NAN ta ruwaito cewar Shugaba Buhari zai wuce kassar Ghana kai tsaye daga jihar Taraba domin halartar bikin murnar cikar kasar shekaru 61 da samun mulkin kai.
NAN