Home Labarai Matsin rayuwa: Ma’aikata za su iya yin rijistar siyan buhun shinkafa kan Naira dubu 40

Matsin rayuwa: Ma’aikata za su iya yin rijistar siyan buhun shinkafa kan Naira dubu 40

0
Matsin rayuwa: Ma’aikata za su iya yin rijistar siyan buhun shinkafa kan Naira dubu 40

A wani yunƙuri na rage tsadar kayan abinci a Nigeria, gwamnatin tarayya ta sanar da shirin siyar da shinkafa mai nauyin 50Kg kan Naira dubu 40 ga ma’aikata.

Acewar wasikar da ta fito daga ma’aikatar ayyuka ta mussaman wacce Daraktan kula da ma’aikata, Jaiyesimi Abimbola ya sanyawa hannu, tsarin siyar da shinkafar zai shafi ma’aikata ne a Abuja.

Wasiƙar ta fayyace matakan da za a bi domin amfana da shirin.

“Duk masu buƙata su cike fom a shafin OHCSF, httpp://www.ohcsf.gov.ng, daga nan sai su fitar da fom din su mika shi ga Daraktan kula da ma’aikata”.

Za a raba shinkafar da biyan kudi ga ma’aikatan da aka sanya domin tabbatar da gaskiya. Shugabannin kungiyoyin ma’aikata zasu sanya idanu kan shirin.

” Kowanne ma’aikaci zai siyi buhun shinkafa daya ne kawai, sannan ma’aikata biyu zasu iya hadawa su suyi buhu 1″, acewar wasikar.

Hakan na zuwa ne bayan sanarwar da ministan yada labarai da wayar da kan al’umma yayi na fara siyar da shinkafar.