Home Labarai Matsin rayuwa: Aiki na ke tuƙuru dan samarwa ƴan Nijeriya mafita mai ɗorewa — Tinubu

Matsin rayuwa: Aiki na ke tuƙuru dan samarwa ƴan Nijeriya mafita mai ɗorewa — Tinubu

0
Matsin rayuwa: Aiki na ke tuƙuru dan samarwa ƴan Nijeriya mafita mai ɗorewa — Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na samar da mafita mai dorewa domin rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a jawabinsa da ya yi wa ƴan kasa kan bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai.

“Ina sane da halin kunci da da yawa daga cikin ku ke fuskanta a cikin waɗannan lokuta masu ƙalubale.

“Gwamnatinmu ta san cewa yawancinku suna fama da tsadar rayuwa da neman aiki mai tsoka. Ina so in tabbatar muku cewa ina jin koken ku,” inji shi.

Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri “yayin da gyare-gyaren da muke aiwatarwa ke nuna alamun nasara, kuma mun fara ganin haske a gaba.”