Home Labarai Matsin rayuwa: Mafi yawan farfesoshi a talauce su ke — Farfesa Audi

Matsin rayuwa: Mafi yawan farfesoshi a talauce su ke — Farfesa Audi

0
Matsin rayuwa: Mafi yawan farfesoshi a talauce su ke — Farfesa Audi

Farfesa Audi T. Giwa, shugaban tsangayar sashen ilimi da ba na kimiyya a jami’ar jihar Kaduna (KASU), ya bayyana cewa yawancin farfesoshi a Najeriya na fama da talauci.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, farfesoshi kadan ne ke iya tuka mota saboda rashin wadataccen albashi da kuma matsalolin tattalin arziki.

Audi ya bayyana hakan ne biyo bayan gabatar da wata maƙala a wani taro da kungiyar ‘Pharmafluence Education Advancement Network (PEAN)’ ta shirya tare da hadin gwiwar jami’ar jihar Kaduna.

Ya ce galibin farfesoshi a Najeriya na ɗaukar albashi kasa da Naira dubu 500 duk wata, amma duk da haka al’umma na kallon su a matsayin masu kudi.

“Mutane nawa kuka sani yanzu wadanda ba za su iya tuka motocinsu ba? Wadannan mutane ne masu arziki; su ba farfesoshi bane, domin mun riga mun talauce. Idan ka ga farfesa yana tuka mota, to suna cikin ƴan kaɗan. Amma duk da haka al’umma na kallonmu a matsayin manyan mutane,” inji shi.

“A ce ni ne na fada a ko’ina—babu wani farfesa a kasar nan da ya ke karbar sama da Naira 500,000 a wata. Wasu suna samun kusan N300,000. Duk da wannan, mutane suna kallon mu a matsayin masu kudi. Idan ku ka ce ba ku da kuɗi, sai su bata rai, wannan ita ce gaskiyar,” in ji shi