
Rundunar Tsaro ta ‘Civil Defence’ a Akwa Ibom ta ce ta samu nasarar kama wani mahaifi, Elisha Effiong ɗan shekara 40 yayin da ya ke yunƙurin sayar da ƴaƴansa mata guda biyu a kan kuɗi naira 700,000.
Kakakin rundunar, Ukeme Umana ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Uyo a jiya Laraba.
Ya ce an cafke mai laifin ne a wani asibiti mai suna Full Care Hospital da ke kan titin Ekpanya a nan Uyo ɗin bayan da wani mai gadi ya tseguntawa rundunar.
Umana ya ƙara da cewa an cafke mahaifin ne a ranar 15 ga watan Nuwamba a daidai ƙarfe 1:15 tare da ƴaƴan nasa Abasifreke Edet ƴar shekara 6 da kuma Rachael Edet, mai shekara 4.
Kakakin ya ƙara da cewa da mahaifin ya shiga hannu, ya faɗawa jami’an tsaro cewa shi a zaune ya ke Adidikim da ke Ƙasar Kamaru.
“Ya kuma baiyana mana cewa wai talauci ne da matsin rayuwa ya sanya shi da matarsa da take can Adidikim ɗin su ka yanke shawarar sayar da yaran,” in ji Umana.
Umana ya ƙara da cewa an kammala binciken farko, inda rundunar za ta mayar da maganar zuwa Hukumar Yaƙi da Fataucin Ɗan’adam domin ta kai shi kotu.