Home Labarai Maulidi: Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

Maulidi: Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

0
Maulidi: Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 16 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin murnar haihuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da babban Sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ya fitar a ranar Juma’a.

Ajani, yayi bayanin cewa, ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya al’ummar Musulmi murna.

Tunji-Ojo ya bukaci al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya da su yi koyi da halayen hakuri da sadaukar da kai.

Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murna, ministan ya nemi al’ummar Musulmi da su yi amfani da damar wajen yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya.