
Hukumar Ƴansandan Farin Kaya, SSS, ta ce ta bankaɗo wani shiri da wasu batagari ke yi na kawo naƙasu wajen bikin rantsuwa da sauran shirye-shirye na siyasa a fadin ƙasar nan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dakta Peter Afunanya ne ya bayyana haka a wata sanarwa danya fitar a yau Alhamis a Abuja.
A cewar sa, shirin da ɓata-garin ke yi na yunkurin dakile kokarin jami’an tsaro na samar da zaman lafiya a kasar ne ta yadda za su haifar da tsoro da fargaba a zukatan yan ƙasa.
“Sabo da haka mu ma jan hankalin ƴan kasa, kafafen yaɗa labarai da kungiyoyi masu zaman kansu da su bi matakan tsaro da aka sanya a yayin tarukan.
“Haka kuma muna kira gare su da su gujewa duk wasu labaran kanzon kurege, raɗe-raɗi da jita-jita, tare da gujewa yin labarai na karin gishiri don kawo rarrabwar kai a kasa,” in ji shi.