
An samu ƙarin wasu mayaƙan Boko Haram sun miƙa kansu ga dakarun Nijeriya a jiya Laraba da safe, inda da yamma kuma dakarun Nijeriya su ka fafata da mayaƙan ISWAP a Malam Fatori.
Kwamndojin Boko Haram da ƴan barandansu ne dai su ka miƙa kansu da ajiye makamai ga dakarun gwamnatin Nijeriya, duk da ISWAP ta yi yunƙurin ta hana faruwar hakan.
Majiyar sirri ta sojojin Nijeriya ta baiyanawa PRNigeria cewa za a samu ƙarin ƴan Boko Haram da za su miƙa kansu zuwa ƙarshen shekara.
“Wasu daga cikin kwamndojin mayaƙan Boko Haram da ƴan barandansu sun tsere daga yankin Jaje a dajin Sambisa, in da tuni su ka miƙa kansu ga dakarun rundunar soji ta 192 da ke Gwoza-Limankara a Jihar Borno.
“Yawancinsu tirsasa su a ka yi su ka shiga Boko Haram lokacin su na ƙanana.
“A yanzu haka sama da mayaƙan Boko Haram 17,000 ne su ka saduda duk da yunƙuri da ISWAP ke yi ta daƙile su daga miƙa kansu,” in ji jami’in tsaron.
Haka-zalika PRNigeria ta jiyo cewa dakarun Nijeriya na nan na fafatawa da mayaƙan ISWAP a daren Laraba a Malam Fatori.
Malam Fatori ya zama yankin da ISWAP ta fi ƙarfi inda har ta kafa ma majalisar shura a yankin wanda ya ke bida da Ƙasar Nijer.