Me ya sa ake ganin cancantar Atiku Abubakar fiye da Buhari a zaben 2019?

0
Me ya sa ake ganin cancantar Atiku Abubakar fiye da Buhari a zaben 2019?

Me ya sa ake ganin cancantar Atiku Abubakar fiye da Buhari a zaven 2019?

Fassarar Rubutun Fidelis Nwagwu

January 25, 2019

Cin hanci da rashawa a cikin kowace irin gwamnati ba baqon abu ba ne, sai dai kowace irin gwamnati da ke mulki da ire-iren qalubalen da take fuskanta game da cin hanci da rashawan. Sai dai ba inda aka fi ganin munin haka kamar  inda a harkar gwamnati ake xora mutane bisa muqamin da ba su cancanta ba ko kuma ware muhimman muqamai domin ‘yan uwa da abokan arziki.

Ba wani abu ba ne sabo ga gwamnatocin Nijeriya su dinga xauko waxanda ba su cancanta ba ko kuma ma ‘yan uwa da abokan arzikinsu na kusa su xora kan wasu muqamai da ake ganin masu maiqo ne, amma a zamanin gwamnatin shugaba Buhari, wannan yanayi na amfani da rashin cancanta ko ‘yan uwantaka wajen gudanar da harkokin gwamnati, tuni ya wuce minsharrin ya kai mahalaqa.Yanzu gwamnatin shugaba Buhari abin da ta sa gaba shi ne watsi da bin dokoki da qa’idoji da cancanta da daidaito a wajen naxin muhimman muqamai, wanda ke nuni da cewa mulki yana nema ya fi qarfinta. A halin da ake ciki yanzu zarge-zarge sun yi yawa ko dai na cin hanci ko rashawa ko rashin amfani da cancanta da shigo da ‘yan uwantaka saboda rashin tsari da kula da gwamnatin ba ta da shi.

To sai dai wani abu da gwamnatin shugaba Buhari ba ta sani ba ko kuma ta sani amma ta take sanin ba yadda za a yi a samu shugabanci nagari ba tare da  an gina qasa bisa tsarin tarbiyantar da al’umma da kawar da cin hanci da rashawa tare da haxin gwiwar ‘yan kishin qasa bisa matakan da suka dace ba.

 A kodayaushe ‘yan kishin qasa a cikin al’umma suna yin da’awar tabbatar da ingantancen tsarin mulki domin sauqaqa wa talakawa, ko ba komai ai gwamnati ko wace iri tana gudana domin inganta rayuwar talakawa ne musamman ganin cewa talakkawan ne ke zaven gwamnatin a bisa tsarin dimokuraxiya. Wannan ne ya sa cikin kowace al’umma ake samun waxanda ba su ganin jariri a bayan mahaifiyarsa sai sun tambayi wanene mahaifin nasa, duk gwamnatin da ta yi watsi da irin waxannan mutane ko kuma ba ta xaukarsu da muhimmanci ko kuma bin shawarwarinsu tana iya samun tarnaqi wajen gabatar da muhimman manufofinta.

Ganin cewa a gwamnatocin bayan na Nijeriya an sha fama da matsalar gudanar da tsarin mulki na rashin ko ‘ yan uwanataka ba wanda ya yi tsammanin hawan gwamnatin shugaba Buhari ta canji a 2015 wannan matsala za ta sake kunno kai. Sai dai kusan shekara huxu bayan nan wace wainar aka toya qarqashin jagorancin shugaba Buhari?

Da hawan gwamnatin shugaba Buhari kan mulki aka fara zargin shugaban sojojin Najeriya a wancan lokaci Janar Azubuike Ehejirika kan handama da babakere alhali shi kuma ya amshi ragama ne daga Janar Abdulrahaman Dambazau, wanda ke nuni da cewa idan Janar Ehejirika yana da hannu cikin waccan damalmala to haka ma Dambazau in har a kwai gaskiya a cikin bayanan kwamitin binciken da gwamnatin shugaba Buhari ta sa a yi a kan kuxaxen makamai, har yau xin nan ba wanda ya kama Janar Dambazau domin hukunta shi, uwa uba yanzu Janar Dambazau yanzu minista ne a gwamnatin shugaba Buhari. Abubuwa biyu suka bayyana daga wannan badaqala, na farko tun da Dambazau na cikin gwamnati zai iya hana hukumomi masu bincike irin EFCC gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. A tuna fa Janar Dambazau ya tava riqe muqamin ministan ma’aikatar harkokin ‘yan sandan Nijeriya da kuma ta cikin gida. Na biyu lallai akwai alamun cewa gwamnatin shugaba Buhari dodorido ce ko kuma angulu da kan zabo, domin bisa dukkan alamu ba Buharin ne ke jan ragamar mulkin qasar nan ba, rahotanni da za a iya gani a cikin jaridu da dama kamar ta Sahara Reporters ta watan Yuli 2016, ta ruwaito wani xan siyasa Dakta Junaid Muhammad yana iqirarin cewa wasu ne ke mulki ba Buhari ba. Cikin su kuwa akwai Mamman Daura wanda yake xan uwan shugaba Buhari ne, shi kuma Mamman Daura shi ya reni Abba Kyari, wanda yake qusa ne a gwamnatin shugaba Buhari. Akwai kuma cikin na hannun daman shugaba Buhari a fadar Aso Rock, wanda shi ma suriki ne ga Mamman Daura. Haka kuma akwai wani minista daga jihar Sakkwato da aka zavo da qarfi da yaji duk da al’ummar jihar sakkwaton ba sa so, amma da yake xa ne ga qanwar Mamman Daura dole aka naxa shi kuma kowa ya yi tsit. Haka Kuma an ga dogarin shugaba Buhari da ake kira kanar Abubakar wanda yake auren jikanyar Buhari. Har wa yau ministan harkokin kuxi ita ma ‘yar uwa ce ga Nasir El’Rufa’I, wanda shi ma ba sai an faxa ba na hannun daman shugaba Buhari ne. Shi kuwa ministan harkokin babban birnin tarayya Abuja, ya sami muqamin ne saboda babansa aminin Buharin ne na tsawon shekaru. Akwai wani mai taimaka wa shugaba Buhari da ake kira Sabi’u Yusuf ko kuma Tunde, wanda shi ma jika ne a wajen shugaba Buhari, kamar yadda Dakta Muhammed ya ruwaito.

Idan aka koma kan batun Hajiya Amina Zakari wadda ta tava riqe shugabanci hukumar zave ta qasa, za a ga qazantar lamarin baki xaya. Tun da farko dai Amina Zakari kwamishina ce a hukumar zaven ta qasa a zamanin shugaba Jonathan, amma Buhari ne ya bada sunanta don wakilci yankin arewa maso yamma, nan ma Buhari ya rasa wanda zai zava in ba ‘yar uwarsa ba daga duk wannan faffaxan yanki. Wannan ne ya sa ko da aka naxa Amina Zakari ta kasance mai kula da tattara da qididdige quri’un zaven 2019 ya sa mutane suka nuna rashin goyon bayansu, domin ganin za ta iya yin amfani da wannan dama ta taimaka wa xan uwanta a wajen zaven.

Daga xan abin da muka yi nazari za a ga munin irin wannan abu da shugaba Buhari ke nema ya yi domin ba a tava ganin inda wani shugaba ya zavi wani makusancin sa ba domin gudanar da zaven da shi kansa yana cikin ‘yan takara ba, ba wannan kaxai ba, a halin da ake ciki qanin Amina Zakarin shi ne ministan harkokin ruwa na Nijeriya duk a qarqashin mulkin gwamnatin Buhari. Saboda haka daga waxannan misalai da ma wasu da ba a kawo ba ta tabbata babu gwamnatin da aka tava yi da take yin naxe-naxe na manyan muqamai ta hanyar rashin cancanta ko kuma ta amfani da ‘yan uwantaka kamar gwamnatin shugaba Buhari. Ke nan babu abin da ya dace a halin yanzu sai ‘yan Nijeriya su yi watsi da gwamnatin shugaba Buhari don kawar da wannan mumunan tsari na gwamnatina da ta ‘yan uwana ko abokai, wanda in ba a yi hankali ba zai iya jagwagwala lamurran mulki da ci gaban qasa da xabbaqa rashin adalci a tsakanin al’umma.

Fidelis Nwagwu ya rubuta daga Abuja