Home Wasanni Messi da wasu ƴan wasa 3 na PSG sun kamu da korona

Messi da wasu ƴan wasa 3 na PSG sun kamu da korona

0
Messi da wasu ƴan wasa 3 na PSG sun kamu da korona

 

Dan wasan gaban PSG, Lionel Messi da wasu ƴan wasan ƙungiyar sun kamu da korona, kamar yadda kungiyar da ke buga gasar Ligue 1 ta sanar.

Bayan Messi, ɗan bayan kungiyar Juan Bernat, mai tsaron ragar ta mai jiran gado, goalkeeper Sergio Rico da kuma ɗan wasan tsakiya Nathan Bitumazala ma sakamakon gwajin da a ka yi musu yankuna cewa su na ɗauke da cutar ta korona.

PSG ta ce ƴan wasan huɗu ma can a killace kuma su na ƙarƙashin tsarin dokokin lafiya.

Faransa ta sanar da samun sabbin masu ɗauke da korona guda 219,126 a jiya Asabar, kuma wannan shine kwana na huɗu a jere a na samun masu ɗauke da cutar sabbi da su ka haure dubu 200.