
Daga Habu Dan Sarki
Wani maciji da ake kyautata zaton sihirtacce ne ya shiga ofishin kula da harkokin kudi na hukumar shirya jarabawar neman shiga jami’a da sauran manyan makarantu ta JAMB dake garin Makurdi babban birnin jihar Binuwai, inda ya cinye tsabar kudi zunzurutu har naira miliyan 36.
Kafin yanzu, masu shirin jarabawar neman shiga Jami’a ko duba sakamakon jarabawar su sai sun sayi kati da ake gogewa a dauki wasu lambobi wato scratch card, a ofisoshin JAMB da ke sassan kasar nan, amma magatakardar hukumar, Ishaq Oloyede ya dakatar da wannan harka.
Wannan shi ya sa aka kafa wata tawagar masu binciken kudi ba musamman da aka tura ofisoshin JAMB da ke fadin Nijeriya, domin gudanar da bincike game da camamar da aka yi ta sayar da kati, don a hada lissafin abin da aka sayar da wanda ba a sayar ba, da kuma hada kudin da aka tara na tsawon lokacin da aka sayar.
Isar wadannan jami’an hukumar masu binciken harkar sayar da kati ofishin JAMB da ke Makurdi a jihar Binuwai, sai jami’ar da ke kula da sayar da katin, Philomina Chieshe ta shaidawa shugaban tawagar sa jami’an sa cewa, ba za ta iya ba da lissafin yadda aka yi da naira miliyan 36 na cinikin da aka yi ba baya bayan, kafin a dakatar da sayar da katin.
Bayan an takura mata da bincike, Philomena ta amsa cewa, mai aikin gidanta ne ta hada baki da wata ma’aikaciyar hukumar Joan Asen suka yi amfani da sihiri suka sace kudin daga ma’ajiyar da ta boye a ofishin ta
A cewar ta, “Ina daya daga cikin masu sayar da kati mutum 4 da ake da su a nan ofishin JAMB na Makurdi. Aikina shi ne in sayar da kati kawai, amma ba ajiyar kudi ba. Abokiyar aikina Joan Asen da wasu manyan jami’an ne suke ajiye kudin. Ni dai kawai duk lokacin da na gama sayar wa zan hada kudi da katin in mika musu.
“Bayan wasu watanni da suka gabata, an zargi ofishin JAMB na Makurdi da laifin almundahanar kudade, inda har aka turo wasu masu bincike daga Abuja, wadanda suka gano bacewar wadannan kudade. Kuma an gane cewa, wata jami’ar kula da kudade Joan Asen da hadin bakin wata da ba ma’aikaciya ba sune suka aikata wannan barnar.”
Philomina ta ce, Joan ce ta shaida musu cewa ita da daya abokiyar hadin bakinta sune suke sace kudin ta hanyar amfani da wani sihirtaccen maciji yana shiga cikin ma’ajiyar kudin yana sato musu.”
A cewar ta, ita ma abin ya dade yana ba ta mamaki yadda za ta ajiye kudi a maboya, amma idan ta bude sai ta ga babu, kuma idan ta kai banki lissafin yana rikice mata. Sai da ta matsa da binciken mutanen da ke zaune a gidanta shi ne ta gane sihirtaccen maciji ne ke sace kudin.