
Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu na iya kirkiro sabbin ma’aikatu daga wadanda ake da su, Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya bayyana haka a jiya Alhamis a Abuja.
A jiya ne Gbajabiamila ya mika jerin sunayen ministocin ga majalisar dokokin kasar kuma shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta.
“Shugaban kasa yana da niyyar raba mukamai ko kuma sake fasalin ma’aikatun ta yadda za ku ji labarin sabbin ma’aikatun da babu su a da don cigaban gwamnati.”
A cewar Gbajabiamila, an zabo wadanda aka nada ne bayan da shugaban kasar ya yi ta tantance su.
Ya ce za a aika kashi na biyu mai kunshe da sunaye 13 ga majalisar, inda ya ce hakan na daga cikin tsarin samar da majalisar ministocin gwamnati.
‘’Kamar yadda kuka sani yana da kwanaki 60 daga lokacin rantsar da shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Ya cika wannan bukata ta kundin tsarin mulki ta hanyar gabatar da sunaye 28 a yau.
‘’Kamar yadda wasikar tasa ta bayyana, kuma aka karanta a zauren majalisar, sauran sunayen, ba a tabbatar da adadin su nawa ba, mai yiwuwa kusan 12, watakila 13, za a mika wa majalisar a kwanaki masu zuwa,” in ji shi.