
Mohammed Abacha, ɗan tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya, Sani Abacha, ya yi nasarar lashe zaɓen fidda-gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a Kano.
Jami’ar zaɓen, Barista Amina Garba, ta bayyana Abacha a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan da ya samu ƙuri’u 736 inda ya ka da Jafar Sani Bello, wanda ya samu kuri’u 710.
Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zaɓukan nasu ne bisa ka’ida tare da sahihan wakilai da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ƴan sanda da jami’an tsaro na jihar ke kula da su.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa jami’an INEC shida ne su ka sanya ido a zaɓen, waɗanda su ka haɗa da mataimakiyar darakta mai kula da zaɓe da sa ido kan jam’iyyu a shelkwatar INEC, Hauwa Hassan; Sakataren gudanarwa na jiha, Garba Lawal; Shugaban sashin shari’a, Suleiman Alkali; Shugaban ayyukan zabe, Sule Yaro; Shugaban Rijistar ICT/Voter Rejistar Ocheka Edwin da; Shugaban kudi kuma Admin, Hassan Dalhatu.