
Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi alla-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da gwamnatin Jihar Borno ta yi.
A cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.
Ya kara da cewa suna yin duk abin da ya kamata wajen ganin an bude sakatariyar jam’iyyar da aka garkame.
Lamarin na faruwa ne yayin da Kwankwason ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.
BBC