
Jam’iyyar NNPP, ta ce ta yi murnar karɓar Sanata Ibrahim Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya tare da ɗumbin magoya bayansa a hukumance.
Dakta Boniface Aniebonam, wanda ya kafa NNPP kuma shugaban ta ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Legas.
Shekarau, tare da magoya bayansa a ranar Laraba, ya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
Shekarau, wanda ya alakanta ficewar tasa da zargin an ajiye shi a gefe, ya ce yana da tabbacin komawa majalisar dattawa a karo na biyu a ƙarƙashin NNPP.
Aniebonam ya ce jam’iyyar ta ji daɗin kwararowar manyan ‘yan Nijeriya zuwa cikinta.
Ya ce: “Haka kuma, muna maraba da Sen. Shekarau da mabiyansa da sauran masu son shiga jam’iyyar NNPP.
“Duk da haka, mu na nan a kan bakar mu cewa masu son shiga cikin jam’iyar mu dole ne su yi imani da gwagwarmayar samar da sabuwar Najeriya da mu ke fata.
A cewarsa, jam’iyyar NNPP za ta tabbatar da an yi wa dukkan mambobinta adalci a zabukan fitar da gwani na jam’iyyar.
Wanda ya kafa jam’iyyar ya ce tuni jam’iyyar ta fara tattaunawa da wasu manyan mutane a Kudancin Nijeriya, wadanda za su shiga jam’iyyar nan ba da jimawa ba.
Ya ce za a sanar da ko su wane waɗannan man ƴan Nijeriyan a hukumance da zarar an kammala tattaunawar da su.