Home Labarai Mun gano wani sabon nau’in ƙwayar cutar maleriya a Arewacin Nijeriya — NIMR

Mun gano wani sabon nau’in ƙwayar cutar maleriya a Arewacin Nijeriya — NIMR

0
Mun gano wani sabon nau’in ƙwayar cutar maleriya a Arewacin Nijeriya — NIMR

 

 

 

Farfesa Babatunde Salako, Darakta Janar na Cibiyar Nazarin Magunguna ta Ƙasa, NIMR, a jiya Litinin ya bayyana cewa cibiyar ta gano wani sabon fitinannen nau’in ƙwayar cutar zazzabin cizon sauro, wato maleriya, mai suna anopheles stephensi a Arewacin Nijeriya.

Salako, wanda ya zanta da manema labarai a Legas yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa da wasu ma’aikatansa suka shirya, ya ce sabon bincike ne a ka yi har aka kai ga gano nau’in cutar.

Ya ce, fitinanniyar nau’in ƙwayar cuta ce mai wuyar kawar da ita, inda ya ƙara da cewa ba a same ta a ko ina a kusa da yammacin Afirka ba.

Ya ce wannan wani bincike ne da masu bincike na NIMR suka yi, kuma hakan yana da tasiri wajen magance zazzabin cizon sauro a Nijeriya.

Salako ya ce a halin yanzu NIMR na binciken kan allurar rigakafin nau’in.

“Mun yi nazari da yawa kan allurar rigakafi kuma muna duban ci gaban rigakafin.

“Muna aiki tare da kungiyoyi biyar a cikin haɗin gwiwa don samar da allurar rigakafi ta gida da za ta bazama a faɗin duniya, wacce ta bambanta da wa ce a ka ssba samarwa,” in ji shi.