Home Labarai Mun kama masu laifi 245 a kwanaki 40 a Kano — Ƴan Sanda

Mun kama masu laifi 245 a kwanaki 40 a Kano — Ƴan Sanda

0
Mun kama masu laifi 245 a kwanaki 40 a Kano — Ƴan Sanda

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama ɓatagari da a ke zargin su da aikata manyan laifuka su 245 a kwanaki 40 da su ka gabata.
Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a shalkwatar rundunar a ranar Alhamis.
Ya ce kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin da rundunar ta ke yi na yaƙi da aikata laifuka a faɗin jihar.
“A ƙoƙarin mu na samar da zaman lafiya ga al’umma, mun dage wajen samar da zaman lafiya a cikin al’umma tare da haɗin kan su. Mu na amfani da bayanan sirri da kuma sintiri, mu yi gaggawar kai ɗauki in da a ka kira mu idan matsala ta afku, mun aiki daidai da yadda ƙa’idojin aikin ƴan sanda ya ke a doka, mu na haɗa kai da sauran hukumomin tsaro, sannan kuma mun yi riƙo da Sintirin nan na Kan ka ce kwabo wanda mu ke ganin alfanon sa sosai,” in ji Kwamishinan.
Da ga masu laifukan da rundunar ta kama a kwai ƴan fashi, masu garkuwa da mutane, ɓarayin shanu, ɓarayin mota, ƴan daba da kuma ƴan shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Haka-zalika rundunar ta sanar da kuɓutar da mutane 6 da ga hannun masu garkuwa da mutane.