Home Labarai Dakarun mu sun kashe kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji 300 – Tinubu

Dakarun mu sun kashe kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji 300 – Tinubu

0
Dakarun mu sun kashe kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji 300 – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin sa na samun nasara a yakin da take da ‘yan ta’addan Boko Haram dake addabar Arewa maso gabas da ‘yan fashin daji dake Arewa maso yamma.

A jawabin da yayiwa ‘yan Nijeriya a bikin ranar ‘yancin, shugaban kasar ya ce kafin ya hau karagar mulki watanni 16 da suka gabata, kasar nan na fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro.

Shugaban kasar wanda ya ce, garambawul din da ake yi ya zama dole don sai ta kasar, yayi nuni da cewa “Mun yanke shawarar yin garambawul ga tsarin tattalin arzikin mu da tasawirar tsaro”.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ta kashe manyan kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji inda ya kara da cewa sojoji sun kashe sama da kwamandojin Boko Haram da ‘yan fashin daji 300 a Arewa Maso Gabas da Arewa maso yamma.