Home Siyasa 2023: Mun yi kura-kurai a baya amma lokaci ya yi na mu gyara- PDP

2023: Mun yi kura-kurai a baya amma lokaci ya yi na mu gyara- PDP

0
2023: Mun yi kura-kurai a baya amma lokaci ya yi na mu gyara- PDP

 

Jam’iyar adawa ta PDP ta amince da cewa ta tafka kura-kurai a lokacin mulkinta na shekaru 16 da ta yi a kan mulki a Nijeriya.

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban jam’iyar, Sanata Iyorchia Ayu ne ya baiyana haka a taron da ya yi da ƴan jarida a jiya Alhamis a Abuja, bayan kammala taron bita da ilmantar da sabbabin shugabanin jam’iyyar PDP na kwanaki biyu da jam’iyar ta shirya.

Shugaban ya amince da cewa tabbas a baya PDP ta tafka kura-kurai, wanda hakan ne ya sanya yanzu ta farka don ganin ta ceto Nijeriya da ƴan Nijeriya da ga waɗanan matsalolin da suke damunsu.

Sanata Ayu ya baiyana cewar, aikin gyaran matsalar Nijeriya yafi ƙarfin mutum ɗaya ko wani ɓangare, in da ya ce “dole ne a taru a haɗa kai don ceto ƙasar da ga wargajewa a sakamakon mulkin ganin dama da rashin tabbas na jam’iyyar APC da ya janyo koma+baya da rashin ci gaba a kasar.”

Ya ce, shugabanni na da muhimiyyar rawa da ya dace su taka don ganin an tayar da komaɗar ƙasar nan da sake mata fasali, ganin yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ke ƙoƙarin mayar da ita a matsayin mabaraciya da rashin makoma da haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin yan ƙasa.

“Najeriya ta zama juji na matsaloli da kuma komawa tamkar mabaraciya duk da arziki da damar da Allah Ya huwace mana, sakamakon irin Mulkin kama karya da na rashin hikima wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa ta APC suka haddasa” inji Iyorchia Ayu.

Haka ma yace aikin mu a matsayin Shugabannin Jam’iyyar PDP a yanzu yana da matukar bukatar samun hadin kai, fatan alheri da kuma gaskiya don ceto kasarnan daga mummunan yanayi na rashin tabbas, kalubale da barazana tsaro da sauran ababen dake iya janyo lallacewa kasarmu baki daya.

“Kowane dan Najeriya yana da kyau ya mayar da hankali ga abin da zai amfanar da kasa a maimakon kara haddasa matsala da zata wargaza hadin kai da ci gaban mu” inji Sanata Ayu.

Daily Nigerian Hausa