
Babban Hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar. Taoreed Lagbaja ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba sojoji za su shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
BBC Hausa ta rawaito cewa Lagbaja ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin bikin rufe taron babban hafsan sojin kasa na uku na 2024, ranar Alhamis a Uyo.
Kwanaki biyar, manyan hafsoshi na Hedikwatar Sojoji, Kwamandojin Ayyuka, Kwamandojin Makarantun Sojojin Najeriya da manyan Cibiyoyin Soji,a fadin kasar nan sun hadu. A Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Taron ya baiwa mahalarta damar tantance yadda ake gudanar da ayyukan sojojin Najeriya, horarwa, da sauran ayyukan da suka shafi aiwatar da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Da ya ke jawabi a wajen rufe taron, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya tabbatar da cewa sojojin ana kan hanyar samun nasara kan rashin tsaro a kasar.
A cewar sa, an tabbatar da hakan ne a bisa bayanan tsaro da ya samu daga rundunonin soji da kuma umarni daban-daban a fadin kasar nan.