Home Labarai Mun kwashi shekaru mu na yi wa Kwankwasiyya hidima amma ba a baiwa ko mutum ɗaya takara a cikin mu ba — R-APC

Mun kwashi shekaru mu na yi wa Kwankwasiyya hidima amma ba a baiwa ko mutum ɗaya takara a cikin mu ba — R-APC

0
Mun kwashi shekaru mu na yi wa Kwankwasiyya hidima amma ba a baiwa ko mutum ɗaya takara a cikin mu ba — R-APC

Ƴan ƙngiyar magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya, da su ka yi mata laƙabi da R-APC sun koka kan yadda jam’iyyar ta fitar da ƴan takara a zaben kananan hukumomi mai zuwa a Kano ba tare da an baiwa ko mutum ɗaya daga cikin su takara ba.

R-APC, wacce aka kafa tun 2018, na daya daga cikin ƙungiyoyin da ke nuna goyon baya ga tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya tun ya na jam’iyar APC a daidai lokacin da aka rigimar sa da Abdullahi Umar Ganduje ta yi ƙamari.

A yayin zantawa da Daily Nigerian Hausa, Ciyaman din R-APC, Sa’idu Yahaya Adam, ya bayyana mamakinsa kan tsarin da jam’iyyar NNPP ta bi wajen fitar da ‘yan takarar.

“Abin al’ajabi ne tattare dani mussaman a wannan jiha tamu mai albarka, a karkashin wannan ƙungiya ta R-APC Kano state mu ka yi al’ajabin abinda ya faru a fitar da ƴan takara da aka yi nasa Kansiloli a wannan jiha ta mu.

” Mun tashi da alhini da takaici halin da muka tsinci kanmu”, inji shi.

Sa’idu Yahaya, ya ce a baya jagorori sun yi musu alkawarin cewa ba yadda za a yi su wulakanta sai dai ba a sanya musu ko mutum daya ba a cikin ‘yan takara na kansila.

Kungiyar wacce ta ce tun 2018 suke kan tsarin Kwankwasiyya sun roki jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanya baki kan abinda aka yi musu.

A makon da ya gabata ne dai jam’iyyar NNPP ta fitar da ‘yan takara a zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai kamawa a jihar Kano.

Sai dai a wata hira da ya yi da Freedom Radio, shugaban NNPP na jiha, Hashimu Dungurawa ya ce duk wanda ya ke da korafi ya rubuto kuma idan aka duba aka ga ƙorafin nasa a kan gaskiya ya ke to za a bi masa hakkin sa.