Home Labarai Mun yi nasarar shari’o’i sama da 3,000 a watanni 11 — EFCC

Mun yi nasarar shari’o’i sama da 3,000 a watanni 11 — EFCC

0
Mun yi nasarar shari’o’i sama da 3,000 a watanni 11 — EFCC

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ta ce ta yi nasara a shari’o’i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin watanni 11 na shekarar 2022.

BBC Hausa ta rawaito cewa, Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ƙwace kuɗi naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ƙasa waɗanda suka mayar wa gwamnati.

Kazalika, EFCC ta ƙwace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) – tsohon mataimaki na musamman ga tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki.

“Haka nan, mun yi nasarar ƙwace kadara 40 a Najeriya da Amurka da Landan da Dubai mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu,” in ji shi.

Mako biyu da suka wuce, wata kotu ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace wasu kadarori biyu na tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison- Madueke.