Home Labarai Mun rufe sansanonin ƴan gudun hijira ne sabo da ana aikata laifuka a ciki — Zulum

Mun rufe sansanonin ƴan gudun hijira ne sabo da ana aikata laifuka a ciki — Zulum

0
Mun rufe sansanonin ƴan gudun hijira ne sabo da ana aikata laifuka a ciki — Zulum

 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce gwamnati ta rufe sansanonin ƴan gudun hijira ne sabo da an maida su wajen aikata laifuka.

Zulum ya faɗi hakan ne a saƙon shi na sabuwar shekara a ranar Asabar.

A tuna cewa a watan Oktoban da ya gabata ne Zulum ya sanar da rufe sansanonin ƴan gudun hijira da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno da ga ranar 31 ga watan Disamba, 2021.

Ya ce babu wata gwamnati da za ta amince a riƙa aikata irin baɗalar da a ke aikatawa a sansanonin, inda ya ƙara da cewa an rufe su ne domin kare martabar yan gudun hijira.

“Mun rufe ne domin mu tsaftace guraren mu kuma baiwa al’umma martabar da kare musu mutuncin su.

“Ba wai saɓawa mu ka yi da rayuwar sansanin ƴan gudun hijira ba, ba kuma so muke mu zauna a nan ba.

“Sabo da haka mu mun yarda da cewa rayuwa mai mutunci ita ce ta fi dacewa da alummar jihar Borno, da ma Nijeriya baki daya.

“Sansanonin ƴan gudun hijira sun zama wajen aikata manyan laifukan, wani sa’in ma har da karuwanci, sayar da miyagun ƙwayoyi, dabanci da sauran su. Babu wata gwamnati da za ta bar al’ummar ta su na rayuwar rashin mutunci kuma ta zura musu ido,” in ji Zulum.