
Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta sasanta ma’aurata 3,579 a 2021, in ji Kwamnadan ta na jihar, Ibrahim Ɗahiru.
Ɗahiru ya baiyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NAN, a Dutse a yau Alhamis.
Kwamnadan ya yi bayanin cewa hakkin hukumar ne ta sasanta ma’aurata.
Ya kuma baiyana cewa Hukumar ta sasanta tsakanin ƴan kasuwa 41, iyaye da ƴaƴan su 221, maƙwabta 319 and manoma da makiyaya 71.
“Sasanta tsakanin al’umma abu ne mai amfani da ya ke wanzar da zaman da soyayya da zaman lafiya a cikin al’umma.
“Hukumar ta na da kwararrun jami’ai da su ka ƙware wajen sasanta al’umma a lokacin da su ka samu saɓani.
“Ina son na yi amfani da wannan dama na tunatar da al’umma cewa Musulunci ya yi horo da sasanta tsakanin al’umma.
“Har gwara ma al’umma su sasanta a tsakanin su ba wai sai an je kotu ba,” in ji shi.