Home Siyasa Mun sasanta Ganduje da Shekarau – Kwamitin Sulhu

Mun sasanta Ganduje da Shekarau – Kwamitin Sulhu

0
Mun sasanta Ganduje da Shekarau – Kwamitin Sulhu

 

Kwamitin sulhu da Jam’iya mai mulki, APC ta kafa domin ya sasanta tsakanin ɓangarorin da su ke rikici da juna a cikin jam’iyar ya ce ya sasanta tsakanin ɓangaren gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje da na tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau.

A makon da ya gabata ne a ka ƙaddamar da kwamitin wanda zai yawata cikin ƙasar nan domin ya sansanta ɓangarorin da ke rikici, in da kwamitin ya sanar da cewa ta Kano zai fara aiki da ga Litinin ɗin da ta gabata.

A na cikin haka kuma sai wata kotu a Abuja ta ce ta rushe shugabannin jam’iya na tsagin gwamna Ganduje ta kuma tabbatar da na ɓangaren Shekarau.

Amma a wata sanarwa da ke yawo a kafafen sadarwa, Shugaban Kwamitin, Sanata Abdullahi Adamu ya ce bayan daguwar ganawa da ya yi da ɓangarori biyu da su ke rikici a jihar, an samu sulhu tsakani.

Sanarwar, wacce babu saka hannun kowa a jiki, ta ce ɓangarorin biyu, wato na Ganduje da na Shekarau, sun tattauna tare da ƴan kwamitin, inda har a ka warware matsalolin da su ka afku.

Sanata Adamu, in ji sanarwar, ya ce amma ba a tattauna a kan wasu batutuwa ba sakamakon su na gaban kotu, inda ya ce gudun yinwa kotu rashin ɗa’a.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yayin zaman sulhun, ɓangarori biyun sun tattauna a kan yadda za a yi wa tufkar hanci, a tabbatar da an tafi da kowa sannan a riƙa baiwa kowanne ɗan jam’iya hakkinsa.

Daily Nigerian Hausa