Home Labarai Mun shigo da kayan aikin noma na biliyoyin naira don yakar yunwa — Tinubu

Mun shigo da kayan aikin noma na biliyoyin naira don yakar yunwa — Tinubu

0
Mun shigo da kayan aikin noma na biliyoyin naira don yakar yunwa — Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya bayar da umarnin shigo da kayan aikin noma daga kasashen waje a wani bangare na kokarin gwamnatinsa na bunkasa noman abinci da kuma dakile wahalhalun da ke addabar kasar.

Tinubu wanda ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a fadin kasar a ranar Lahadinnan ya kuma ce matakin wani bangare ne na karfafa gwiwar manoma da gwamnati ta yi na kara samar da abinci a farashi mai sauki.

Ya ce, “Muna bayar da kwarin gwiwa ga manoma domin su kara samar da abinci a farashi mai sauki. Na ba da umarnin a cire haraji da sauran harajojin shigo da kayayyaki kan shinkafa, alkama, masara, dawa, magunguna, da sauran kayayyakin nan da watanni 6 masu zuwa, da farko, don taimakawa wajen rage farashin kayayyaki.

“Na yi ta ganawa da Gwamnoninmu da manyan Ministocinmu don hanzarta samar da abinci a Najeriya.Mun rarraba takin zamani,kuma manufarmu ita ce noma fiye da hekta miliyan 10 na fili don noma abubuwan da muke ci.

Yace gwamnatin tarayya za ta ba da duk wani abin da ya dace don wannan shirin, yayin da jihohi ke ba da filayen, wanda zai sa miliyoyin al’ummarmu su samu aikin yi da kuma kara samar da abinci.