Home Ƙasashen waje Mun tattauna batun kisan Khashoggi da Yarima bin Salman na Saudiya – Biden

Mun tattauna batun kisan Khashoggi da Yarima bin Salman na Saudiya – Biden

0
Mun tattauna batun kisan Khashoggi da Yarima bin Salman na Saudiya – Biden

Mun tattauna batun kisan Khashoggi da Yarima bin Salman na Saudiya – Biden

 

Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden ya ce ya taɓo batun kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 2018 “a ganawar da ya yi ranar Jumma’a da Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman da ake kira (MBS) a Jeddah, a rana ta uku na rangadinsa na farko a Gabas ta Tsakiya a matsayinsa na shugaban kasa.

Mista Biden yace “Abin da ya faru da Khashoggi ya yi matukar tayar da hankali…kuma ya bayyana karara, idan wani abu makamaicin haka ya sake faruwa, to zasu maida martani.

Biden yace batun da ya fara tattaunawa da MBS, kenan tun ma kafin zantawarsu ta yi nisa da mutumin da jami’an leken asirin Amurka suka yi imanin shi ya ba da umarnin kisan gillar da akayiwa Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiya dake Turkiya.

Ziyar da Biden ya kai kasar Saudiyya tare da ganawa da Yarima Ben Salman, ta yi hannun riga da alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, na mai da masarautar saniyar ware saboda take hakkin dan Adam.