Home Labarai Mun ƙwace gidaje 97 da rufe asusun banki 1,233 na mutanen da ake zargi da rashawa — ICPC

Mun ƙwace gidaje 97 da rufe asusun banki 1,233 na mutanen da ake zargi da rashawa — ICPC

0
Mun ƙwace gidaje 97 da rufe asusun banki 1,233 na mutanen da ake zargi da rashawa — ICPC
Hukumar yaƙi da ayyukan rashawa a Nijeriya ta ICPC ta ce ta ƙwace gidaje aƙalla 97 daga hannun mutane daban-daban cikin shekara huɗu da suka wuce.
Cikin jerin kadarorin da ta ƙwace akwai gine-gine 33, da filaye, da wata ma’aikata waɗanda hukumar ta ƙwace daga wajen Dr Jimoh Olatunde, tsohon akanta a hukumar shirya jarrabawa ta JAMB.
ICPC ta bayyana wa Jaridar Punch cewa ta kuma garƙame asusun ajiya 1,233 tun daga 2019 zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Bugu da ƙari, 60 daga cikin asusan mutanen da ake zargi da aikata rashawa, an miƙa su ga gwamnatin tarayya.
Asusan na ɗauke da kuɗi naira miliyan N547.7 da kuma dalar Amurka $669,248.89 jimilla.
Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulazeez Yari na cikin waɗanda aka ƙwace wa kuɗin, inda gwamnati ta karɓe masa dala $669,248.89 da kuma naira N24,289,910.89.