Home Siyasa 2023: Muna addu’ar Allah Ya baka nasara, Sarkin Damaturu ya tabbatar waOsinbajo

2023: Muna addu’ar Allah Ya baka nasara, Sarkin Damaturu ya tabbatar waOsinbajo

0
2023: Muna addu’ar Allah Ya baka nasara, Sarkin Damaturu ya tabbatar waOsinbajo

 

Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya ce Masarautar za ta goyi bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo tare da yin addu’a a kan Allah Ya sa ya zama shugaban ƙasa a 2023.

El-Kanemi ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasar wanda ya kai ziyarar ban girma a fadarsa jiya Litinin a Damaturu, Yobe.

Osinbajo ya je Yobe ne a ci gaba da tuntubar sa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaben fidda-gwani na jam’iyyar.

Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban kasar ya kai fadar wata alama ce da ke nuna girmamawar da ya ke da ita ga masarautun gargajiya.

“Abin da muke sa rai shi ne ci gaba; don ɗora wa da ga inda a ka tsaya, kuma da ga nan ne za ku ci gaba.

“Mu na godiya ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari; idan ka kawo batun tsaro, gwamnanmu zai ba da shaida kan abin da ya faru a jihar nan; amma da Buhari ya hau mulki, sai al’amura suka gyaru; abubuwa sun canza, mun samu zaman lafiya.

“Mun shaida zaman lafiya a wannan gwamnati; Shugaba Buhari ya yi aiki sosai a kasar nan mai girma; yana yin abubuwa da yawa duk da kalubale; muna bukatar mu yi godiya ga shugabancin ku.

“Da yardar Allah za mu sa ku a cikin addu’o’i da goyon baya ta kowace fuska don ganin kun yi fice; kuma a karshen wannan rana muna addu’ar Allah Ya sa ka zama shugaban wannan kasa mai albarka Nijeriya.”

A nashi ɓangaren, mataimakin shugaban kasan ya bukaci El-Kanemi da ya godewa gwamnan, wanda a cewar sa, ya kasance abokin tarayya, mai goyon baya da kuma amana; da abin da ya yi wa jam’iyyar.

“Amma a yau, na zo ne domin ganawa da wakilan jam’iyyarmu ta APC, wadanda za su zabi ko za su tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu; dan takarar jam’iyyar mu a zabe mai zuwa a 2023,” in ji shi