
Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, Murtala Sule Garo ya ajiye mukamin sa na Kwamishina domin Cika Umarnin Gwamna Ganduje.
Cikin wasikar ajiye aiki da ya fitar a yau Lahadi, Garo yace ya ajiye mukamin nasa ne domin yana da sha’awar yin takarar Gwamnan Jihar Kano a zabe mai zuwa.
A wasiƙar, Garo ya godewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bisa bashi dama ya yi wa jihar hidima tsawon shekaru bakwai.
“Ina yabawa Gwamna Ganduje bisa damar da ya bani nayin aiki da shi a Matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi.
“Ina godiya da damar da Kuma Sauran abokan aikin da mukai aik da su”. Inji Garo.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa dama dai an dade ana raɗe-raɗin cewa Garo,ai tsaya takarar gwamna a jihar duk da cewa bai taɓa fito wa ya bayyana da kansa ba.
Sai dai kuma murabus ɗin da ya yi a yau zai tabbatar da gaskiyar raɗe-raɗin da a ke yi.
Shima Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Nura Muhammad Dankadai ya yi murabus.
A na raɗe-raɗi cewa zai tsaya takara majalisar Wakilai a mazaɓar taraiyar ta Doguwa da Tudunwada.
Shima kamar sauran kwamishinoni, ya gode wa Ganduje bisa damar da ya bashi a ka fama da shi a gwamnatin.
Idan za’a iya tunawa a safiyar lahadin nan ne aka wayi gari da sanarwar da take Umarni ga masu rike da mukamai a gwamnatin Ganduje da su ajiye mukamansu Matukar suna da sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.