Home Siyasa Musa Iliyasu Kwankwaso ya bi umarnin Ganduje, inda ya ajiye mukaminsa na Kwamishina

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bi umarnin Ganduje, inda ya ajiye mukaminsa na Kwamishina

0
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bi umarnin Ganduje, inda ya ajiye mukaminsa na Kwamishina

 

A wanni da fitar sanarwar da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar na cewa duk wani mai rike da mukamin a gwamnatinsa da ya ke da niyyar tsaya wa takara a zaɓukan 2023 to ya yi murabus, Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara ta Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ajiye mukamin sa.

Da yake Zlzantawa da manema labarai, Kwankwaso ya ce ya ajiye mukamin nasa ne domin yana da sha’awar yin takarar Majalisar Wakilai a mazaɓar Kura/Madobi/Garun-Mallam a zabe mai zuwa.

A cewar sa, shi dama tuni ya ajiye muƙamin nasa a bisa biyayya ga sabuwar dokar zaɓe ta 2022.

Ya ce “Ni dama tun tuni na ajiye mukamina na Kwamishina kamar yadda sabuwar dokar zabe ta bukata. Kawai ban baiyana bane sai yau” inji Kwankwaso.

Tsohon Kwamishinan ya ƙara da cewa ya na fatan zai samu nasara a takarar da zai tsaya a jam’iyyar APC a zaɓukan da za a yi na 2023.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa da asubar yau Lahadi ne a ka wayi gari da sanarwar da ta ke Umarni ga masu rike da muƙamai a gwamnatin Ganduje da su ajiye mukamansu matukar su na da sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.