Home Labarai Mutala Mohammed da kalubalen Shugabancin da Najeriya take fuskanta a yanzu

Mutala Mohammed da kalubalen Shugabancin da Najeriya take fuskanta a yanzu

0
Mutala Mohammed da kalubalen Shugabancin da Najeriya take fuskanta a yanzu
Janar Murtala Mohammed
Daga Abbas Yushau
Yau shekara 42 ke nan da wasu sojoji makiya cigaban tarayyar Najeriya suka kashe tsohon shugaban kasar mu Janar Murtala Ramat Muhammad , lokacin da nake tasowa mahaifina(Allah madaukakin sarki ya kara masa lafiya da tsawon rai) yana da wata  katauwar Kwabet cike da littatafai da Makalu da ya saya ya ajiye wasu a tun a shekarun 1970, wasu kuma a shekarun 1980, hakan yasa idan na shiga dakinsa tun ina firamare nakan zakulo irin wadannan littatfai da mukalu wasu an rubata su cikin harshen turanci, wasu kuma cikin harshen Hausa, na kan karanta na Turancin duk da bana ganewa har na dan fara ganewa, na Hausar kuma  ina ganewa.
Ganin haka yasa ka mun kaunar Janar Murtala Ramat Muhammad sakamakon karanta abinda mahaifina ya saya ya ajiye, akan tsohon wannan dan kishin kasa, daga nan ne kuma na koma da kaina idan naje dakunan karatun kasar nan musamman ma Murtala Muhammad Library nayi ta karance karance akan Janar Murtala Muhammad.
Yau muna 13 ga watan Fabrairu na Shekarar 2018, kuma  a yau ne Janar Murtala ya shekara 42 ke nan da komawa ga mahaliccinsa ,amma tun daga ranar da Janar din ya rasu ,Najeriya take fuskantar kalubalan shugabanci, mutuncin kasar mu koyaushe sai zubewa yake a idan Duniya, cin hanci da rashawa wacce Janar Murtala ya tashi haikan zai yaka ta zamo halak a tsakanin Yan Najeriya, hakika da wannan dantaliki yayi tsawon rai da yanzu kasar mu tana gogayya ne da kasashe irinsu Dubai, da Malaysia,  abinda zai baka shaawa anan shi ne a wata shida kacal da Janar Murtala yayi yi yana mulkin Kasar nan duk da yake cewa matshi ne a lokacin mai jini a jika ya aiwatar da abubwan da wadanda suka shekara 8, ko suka yi, uku ko sukayi 9 basu aiwatar ba, daga cikin babbar gajiyar mulkin Murtala da muke amfana dashi a halin yanzu shi ne birnin tarayya Abuja, yanzu kowanne dan Najeriya yakan je wannan babban Birni namu a saukake yaje ya dawo ba tare da wata tsangwama ba.
Sannan Janar Muratala  Muhammad ya zama abun buga misali a Najeriya da Afrika a matsayinsa na matashi a wancan lokaci saboda kwarjini da Allah yayi masa da kuma kokarin gabatar da Shugabanci babu sani babu sabo.
Lokacin da ya karbi mulkin kasar nan ranar 29 ga watan Yuli na shekarar 1975 tattalin arzikin Najeriya yana mashashra  ,kan kace mene wannan Janar Murtala ya fara kokarin farfado dashi, har ma da yaga talaka Nama yana kokarin ya gagareshi yace ya sa aka shigo da Shanu aka fara yankawa ana sayarwa da talakawa nama, har aka fara kiran naman da suna MURTALAS MEAT musamman ma ga ‘’Yan uwanmu na kudu wadanda suke kamar Kuraye wajen cin nama.
A fagen kwato yancin kasashen Afrika daga danniyar turawan mulkin mallaka ,baa bar wannnan dan taliki a baya ba, wanda masu tattara bayanan sirri suke cewa jawabin da ya yiwa Shuwagabannin kasashen Afrika a gaban zauren kungiyar ta OAU ranar 11 ga watan Janairun 1976 shi ne yasa turawan yammacin Duniya suka kitsa kashe Janar Murtala bayan wata daya da yin wannan jawabi.
Kadan daga cikin abinda Janar Murtala Ramat Muhammad ya shaidawa shugabannin na Afrika , shi ne ya kamata kasashen nahiyar su mike tsaye domin tabbatar da yancin yankin wanda turawan mulkin mallaka suka mamaye.
“ Ya maigirma shugaban wannan taro  duk sanda nayi nazarin akan yadda shaidanun da suka kawo mana banbancin launinin fata a nahiyarmu ta Afrika ,zuciya ta tana zub da jini kuma na tabbata zuciyar duk wani dan Afrika mai kishi na asali zata zub da jinni”
Sannan abun shaawa da juyin mulkin da Janar Murtala ya hau mulki shi ne juyin mulkin da ka fara yi a tarayyar Najeriya ba tare da an harba harsashi ko daya ba ,ko a digar da jinin dan Adam.’’
Janar Murtala ya bar Duniya ya bar wasu daga cikin manyan kasar nan domin su gaje shi su dora kasar akan turba amma duk sai suka ci amanarsa.
Daga cikin magadan Janar Murtala Muhammad akwai ,Janar Olusegun Obasanjo da Janar Muhammadu Buhari da Manjo Janar Shehu Musa Yar’adua, da Janar Theophilus Yakubu Danjuma da Janar Ibrahim Badamasi Babangida , amma bayan rasuwarsa wadannan mutane duk sai suka ajiye manufofin da Janar Murtala ya dora kasar nan akai.
Muna kyautatawa Marigayi Murtala Muhammad zatao saboda kashe shi akayi wadanda kuma suk aikata wannan ta’asa tana wuyansu, kuma ya rasu ranar Jumaa ,wacca baa ma tambayar kabari.
Mutum ne  da yayi riko da Addinisa na musulunci fiye da yadda ba’a zato, saboda jaruntar  Janar Murtala da shahara da yayi kuma ya fito daga Jahar Kano zakaga al’umma da dama suna yiwa wannan gari bakin ciki wai cewa Murtala bama dan Kano bane ,wanda zuki ta malla ce idan kuma suna  da jayayya akan abinda na fada suje su tambayi sannan nan malamin nan mai bincike Malam Ibrahim  Ado Kurawa wanda ma suna da alaka da marigayin.
Zan rufe da wani baiti daya da babban Malami marigayi Sheikh Dr Aminuddin Abubakar ya rubuta akan  Marigayi Janar Murtala, Allah ya jikansu gaba daya.
‘’ Maki gudu sa gudu Gunduma kwanya shugaba Murtala”