
Akalla mutane 15 aka tabbatar da cewar sun mutu yayin da mutane 55 suka ji munanan raunuka a wani mummunan harin Bom da Boko Haram suka kai ranar ;ahadi da daddare a yankin Bale dake wajen garin Maiduguri.
Kamfanin dillancin labarai na Najeiya, NAN, sun ruwaito cewar an jiho karar harbe harben bindiga da kuma fashewar wasu abubuwa masu karfi wanda aka dauki a wanni ana jiyo wannan kara a yammacin ranar Lahadi daga wajen garin Maiduguri.
Wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewa maharan sun kai wannan hari ne a yankunan bale-Shuwa da Bale-Kura wanda suke gab da cikin garin Maiduguri da misalin karfe 8 na maraice.
Majiyar ta cigaba da cewar, maharan sun ajiye motocinsu taku kadan daga shingen jami’an tsaro, inda suka sadada zuwa yankin da zasu kai harin.
Haka kuma, majiyar ta cigaba da cewa, ba tare da wani batala lokaci ba jami’an tsaro suka shiga musayen wuta tsakaninsu da maharan, wanda suka dinga tayar da abubuwa masu fashe da karfin gaske.
“Da yawan mutane ciki har da mata da kananan yara sun jikatasakamakon raunukan da suka ji a yayin da ake harbe harbe”
“Sabida tsananin duhu a lokacin, ba’a iya dauke gawarwakin mutane nan take ba, saboda akwai masu shirin kai harin kunar bakin wake a cikin maharan”
Haka kuma, Kwamandan rundunar Lafiya Dole Manjo Janar Rogers Nicholas ya karyata cewar an samu hasarar rayuka daga bangaren rundunar sojin Najeriya ko fararen hula.
A lokacin da yake maida martani ga NAN a sakon tes da ya aike musu, yace mutanan da aka kashe dukkansu ‘yan Boko Haram ne.
“Ba gaskiya bane. lallai an kawo hari, kuma tuni sojanmu suka mayar da wuta inda suka kashe ‘yan Boko Haram”
“Bayan haka kuma, ‘yan kungiyar Boko haram sun zo tare da ‘yan kunar bakin wake, wanda suka dinga tayar da bamabaman da suka layyace jikinsu da shi a lokacin da suke guduwa bayan da soja suka bude musu wuta”.
NAN