
Akalla mutane 22 aka tabbatar da rasuwarsu, yayinda wasu 28 suka samu manyan raunuka a wani mummunan harin bom din da aka kai a tsakiyar kasuwa a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, lamarin ya auku ne a ranar juma’a da misalin karfe 9 na dare, inda wasu mutum uku da suka layyace jikinsu da kayan fashewa suka tayar da bom din a kasuwarkifi dake bayan garin Konduga.
Wani da abin ya faru akan idonsa, Idrissa Bana, ya bayyana cewar, daya bayan daya mutum ukun da suka layyace jikinsu da bom din suka dinga tayarda shi, a lokacin da jama’a suka cika ana tsaka da hada hada a cikin kasuwa.
Bana ya cigaba da cewar, akalla mun ga gawar mutum 22 yayin da kuma aka samu mutane kusan 28 da suka samu munanan raunuka, ya kara da cewar, tuni aka kwashe wadan da suka ji raunuka zuwa asibiti a cikin garn Maiduguri.
“Akwai mutane da yawa a lokacin da ake gab da rufe kasuwar da suke hada hada, inda ‘yan kunar bakin waken suka yi sa’ar shigo tsakiyar mutane suka tayar da bomm din da ke jikinsu”
Wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar wannan al’amari, ta kara da cewar, daga zarar an gama tantance bayanai kan wadan da suka kai wannan hari da kuma samun alkalumanwadan da suka rasu da wanda suka jikkata za’a bayyanawa manema labarai.