Home Labarai Mutane 800 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kwara

Mutane 800 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kwara

0
Mutane 800 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kwara

Daga Hassan AbdulMalik

Mutane sama da 800 ne suka sauaya sheka daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa babbae jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kwara.

Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kwara, Iyiola Oyedepo ne ya karbi gungun masu sauya shekar daga APC zuwa PDP a yau Juma’a a wajen taron shugabannin zartarwar jam’iyyar na shiyyar arewa ta tsakiya da jam’iyyar ta gudanar a yau.

Dakta Hanafi Alabere, wanda shi ne ya jagoranci gungun masu sauya shekar daga mazabar Alanamu da ke a karamar hukumar Ilorin ta yamma, ya bayyana cewa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba na jam’iyyar APC, shi ne ya sanya suka yanke hukuncin barin jam’iyyar zuwa PDP.

Shugaban jam’iyyar PDP ta jihar Kwara, Oyedepo ya bayyanawa shugabannin shiyyar arewa ta tsakiya cewa babu wani fitaccen dan jam’iyyar PDP a jihar Kwara da ya fita ya bar jam’iyyar zuwa APC tun da APC ta karbi mulki a 2015.

Oyedepo ya bayyana shigowar Alabere da mukarrabansa cikin PDP a matsayin wata manuniya da ke nuna dawowar farin jinin PDP a jihar Kwara.

Shugaban PDP na shiyyar arewa ta tsakiya, Mista Theophilus Dakas, ya yabawa shugabannin zartarwar jam’iyyar bisa kokarinsu na ci gaba da jan ragamar jam’iyyar cikin gogewa duk kuwa da ‘yan matsattsalu da jam’iyyar ta shiga na shugabanci.

Dakas ya ja hankalin ‘yan jam’iyya da su ci gaba da aiwatar da abubuwan da za su dada jawo hankalin mutane zuwa jam’iyyar.

Ya kuma bawa ‘yan jam’iyya tabbacin cewa zamanin karfafa a jam’iyyar PDP ya wuce. Babu batun kakaba wa mutane dan takara ta karfin tsiya a jam’iyyar PDP kuma