Home Lafiya Mutane 189 a ƙananan hukumomi 20 ne su ka kamu da kwalara a Kano

Mutane 189 a ƙananan hukumomi 20 ne su ka kamu da kwalara a Kano

0
Mutane 189 a ƙananan hukumomi 20 ne su ka kamu da kwalara a Kano

 

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta samu adadin wadanda suka kamu da cutar kwalara, wato amai da gudawa a cikin kananan hukumomi 20 da ba su gaza 189 ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya tabbatar da kamuwa da cutar a wani taron manema labarai a Kano a jiya Talata.

Tsanyawa ya ce an sami rahoton mutuwar mutane biyar, yayin da 184 daga cikin wadanda suka kamu da cutar kuma aka yi musu magani kuma sun warke gaba daya.

Ya lura cewa an samu raguwar bullar cutar kamar yadda ya afku a shekarar 2021 inda jihar ta samu mutane 12,116 da suka mutu 329.

A cewarsa, barkewar cutar kwalara ta kaka-kaka ce, inda ya ƙara da cewa cuta ce ta kwayoyin cuta da mutane ke kamuwa da ita mai suna v. cholerae

Kwamishinan ya ci gaba da cewa abubuwan da ke haifar da kamuwa da cutar kwalara sun hada da rashin tsaftar hijira muhalli.