Home Lafiya Mutane biliyan 1 na fuskantar haɗarin kurumcewa sabo da jin kiɗa mai ƙara sosai — WHO

Mutane biliyan 1 na fuskantar haɗarin kurumcewa sabo da jin kiɗa mai ƙara sosai — WHO

0
Mutane biliyan 1 na fuskantar haɗarin kurumcewa sabo da jin kiɗa mai ƙara sosai — WHO

 

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce mutane biliyan 1, ƴan shekara 12 zuwa 35, fuskantar haɗarin kurumce wa sakamakon yawan jin kiɗa da sauran ƙararraki masu ƙarfi sosai.

WHO ta yi wannan gargaɗi ne a wani sabon kundin shawarwari na duniya da ta fitar domin magance matsalar kurumce wa.

Ta ƙaddamar da sabon kundin shawarwari ne domin jin ƙararraki daidai gwargwado a guraren taro ne a wani ɓangare na bikin tunawa da Ranar Ji ta Duniya a yau Alhamis, 3 ga watan Maris.

Taken bikin na bana shine, “ka kula da kunnen ka ka domin ka rayu da jin ka”.

Taken na jan hankalin duk wasu guraren taruka na al’umma inda a ke saka kiɗa mai ƙarar gaske.

Sama da mutane biliyan 1.5 ne su ka kurumce a faɗin duniya, kamar yadda ƙididdiga ta nuna a kwanan nan.

Wannan ƙididdigar za ta iya ƙaruwar zuwa biliyan 2.5 idan ba a yi wasa ba, inda WHO ta baiyana cewa idan a na kula da lafiyar jama’a, to za a iya daƙile kurumcewa da kashi 50 cikin 100.