Home Labarai Mutane 202 cutar korona ta kashe a Oyo, in ji NCDC

Mutane 202 cutar korona ta kashe a Oyo, in ji NCDC

0
Mutane 202 cutar korona ta kashe a Oyo, in ji NCDC

Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC, ta ce kawo yanzu, a kalla mutane 202 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a jihar Oyo.

Dayo Adigun, mai magana da yawun dakin gwaje-gwaje na cibiyar bayar da agajin gaggawa ta jihar Oyo, mai wakiltar NCDC ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a Ibadan.

Adigun ya bayyana haka ne a wani shiri na wayar da kan jama’a da Ilimantarwa da kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC reshen jihar Oyo ta shirya.

Ya ce cibiyar ta gudanar da gwajin cutar COVID-19z wacce aka fi sani da korona, a kan mutane dubu 91,271 a cikin jihar, wanda aka gano dubu 10,156 na dauke da ƙwayar cutar tun daga daga 2020 zuwa yau.

A cewarsa, har yanzu COVID-19 na ci gaba da wanzuwa a jihar Oyo da ma Nijeriya baki daya, amma da gaske mutane ba sa fitowa domin yin gwaji, suna tunanin babu kwayar cutar.

Adigun ya ce a halin yanzu ba a gane karuwar masu dauke da cutar ba, saboda yanzu mutane ba sa fitowa yin gwaji.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su je a yi gwaji domin sanin halin da suke ciki da kuma yin allurar rigakafi don gina garkuwar jikinsu daga kamuwa da cutar.