Home Lafiya Mutane miliyan 60 ne ke fama da ciwon hauka a Nijeriya — Likitan ƙwaƙwalwa

Mutane miliyan 60 ne ke fama da ciwon hauka a Nijeriya — Likitan ƙwaƙwalwa

0
Mutane miliyan 60 ne ke fama da ciwon hauka a Nijeriya — Likitan ƙwaƙwalwa

 

 

Taiwo Obindo, shugaban Kungiyar Likitocin Ƙwaƙwalwa ta Najeriya, APN, ya ce sama da ƴan ƙasar miliyan 60 ne ke fama da ciwon hauka.

Obindo, wanda kuma shi ne shugaban tsangayar koyar da ilimin likitancin ƙwaƙwalwa ta Kwalejin Likitoci na Afirka ta Yamma, reshen Najeriya, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, a yau Lahadi a Abuja.

“Kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa na cikin wani hali ganin cewa muna da ƴan Nijeriya sama da miliyan 60 da ke fama da taɓin hankali daban-daban da kuma yadda kusan kashi 10 cikin 100 ne kawai ke iya samun kulawar da ta dace.

“An bar mu da fiye da kashi 90 cikin 100 da ba za su iya samun kulawa ba kuma ana kiran wannan rukuni tazarar jiyyar taɓin hankali,” in ji Mista Obindo.

Ya ce tazarar ta samo asali ne sakamakon abubuwa daban-daban kamar tazarar ilimin da mutane ba sa samun bayanan da suka dace game da musabbabin kamuwa da taɓin hankali.

Obindo ya ƙara da cewa wasu abubuwan da ke kawo cikas wajen shawo kan cutar taɓin hankali a Nijeriya sun haɗa da camfe-camfe da imani da gargajiya; rashin isassun wuraren kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa da ƙarancin kwararrun lafiyar kwakwalwa.